Zaben Edo: INEC Ta Mika Takardar Shaidar Cin Zabe Ga Okpebholo

Gwamnan jihar Edo mai jiran gado, Monday Okpebholo,

Bikin mika takardar shaidar cin zaben ya gudana ne a shelkwatar INEC dake Abuja a yau Alhamis.

Hukumar zaben mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta mika takardar shaidar cin zabe ga mutumin daya lashe zaben gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, na jam’iyyar APC.

Bikin mika takardar shaidar cin zaben ya gudana ne a shelkwatar INEC dake Abuja a yau Alhamis.

INEC ta ayyana Okpebholo a matsayin wanda yayi nasara a zaben da ya gudanar a ranar Asabar, 21 ga watan Satumbar da muke ciki bayan samun kuri’u 291, 667 inda ya doke dan takarar dake biye da shi, Asue Ighodalo na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 247, 274.

Dan takarar jam’iyyar APC ya samu galaba a fiye da kananan hukumomi 10 daga cikin 18, inda ya bar dan takarar da kwarya-kwaryar nasara a ragowar kananan hukumomin.