Kungiyoyin agaji dake aikin ceto akan iyakar Libiya da Nijar sun sanar da gano gawarwakin bakin haure da suka mutu a cikin hamadar Sahara wadanda alamu ke nuna cewa tsananin kishin ruwa ne yayi sanadin mutuwar su
Yankunan sahara Agadas wadanda suka raba iyakoki da kasashen Libiya da Aljeriya a arewacin Nijar sune su kafi zama mafi hatsarin ga bakin haure dake son shiga Turai
A yan kwanakin nan ana samun yawaitar bakin haure dake mutuwa a cikin hamadar sahara inda kungiyoyin agaji suka sanar da mutuwar bakin haure kusan 50 yayinda suka ceto akalla 200 da aka zubar dasu.
Tun bayan soke dokar haramta safarar bakin haure da gwamnatin mulkin sojin Nijar tayi a shekarar da ta gabata ake samun yawaitar mutuwar bakin haure dake bi ta barauniyar hanya wanda masu jigilar suke zubar dasu a cikin hamada, lamarin da ya sa kungiyar dake aikin jigilar bakin haure yin kira ga gwamnati ta dauki mataki
A saurari rahoton Hamid Mahmoud:
Your browser doesn’t support HTML5