Gasar Olympics: Waldum Ya Zabi Wadanda Za Su Bugawa Super Falcons Wasa

This photograph taken on June 26, 2024 shows the Olympics rings on the Eiffel Tower in Paris, on June 26, 2024. (Photo by OLYMPIA DE MAISMONT / AFP)

Kociyan kungiyar kwallon kafar Najeriya ta mata “Super Falcons”, Randy Waldrum, ya zabi Rashidat Ajibade da mai tsaron raga Chiamaka Nnadozie da mai tsaron baya Osinachi Ohale da ‘yar wasan gaba Asisat Oshoala da wasu mutum 14 a kunshin karshe na sunaye ‘yan wasan da zasu halarci gasar wasannin Olympics ta kwallon kafar mata a kasar Faransa.

Har ila yau kunshin sunayen ‘yan wasan ya hada da na masu tsaron baya Oluwatosin Demehin da Michelle Alozie da ‘yan wasan tsakiya Deborah Abiodun da Halimatu Ayinde da Christy Ucheibe da kuma Toni Payne sai kuma ‘yan wasan gaban da suka hada da Esther Okoronkwo da Chinwendu Ihezuo da Uchenna Kanu.

An tsara cewar tawagar zata bar sansanin samun horon dake Sevilla zuwa Faransa a ranar Alhamis, 18 ga watan Yulin da muke ciki.

Tawagar Najeriya zata fara halartar gasar Olympics ta mata ne a karon farko tun bayan wacce ta shiga a shekarar 2008 a kasar China, inda za ta kara da kasashen Brazil da Sifaniya da Japan a jere, a gasar ta bana.

Tawagar Super Falcons a gasar wasannin Olympics ta bana a birnin Paris:

MASU TSARON RAGA: Chiamaka Nnadozie (mai wasa a kungiyar Paris fc); Tochukwu Oluehi (mai wasa a kungiyar Shualat Alsharqia fc ta kasar Saudiyya)

‘YAN BAYA: Osinachi Ohale (mai wasa a kungiyar Pachucha Club de Futbol ta kasar Mexico) da Oluwatosin Demehin (mai wasa a kungiyar Stade de Reims ta kasar Faransa) da Michelle Alozie (mai wasa a kungiyar Houston Dash ta kasar Amurka) da Nicole Payne (mai wasa a kungiyar Portland Thorns ta Amurka) da Chidinma Okeke (mai wasa a kungiyar Mynavi Sendei Ladies ta kasar Japan).

‘YAN WASAN TSAKIYA: Deborah Abiodun (mai wasa a jami’ar Pittsburgh ta Amurka) da Halimatu Ayinde (mai wasa a kungiyar FC Rosengard ta kasar Sweden) da Christy Ucheibe (mai wasa a kungiyar SL Benfica ta kasar Portugal) da Jennifer Echegini (mai wasa a kungiyar Juventus Ladies ta kasar Italiya) da Toni Payne (mai wasa a kungiyar Sevilla FC ta kasar Sifaniya).

YAN WASAN GABA: Rasheedat Ajibde (mai wasa a kungiyar Atletico Madrid FC ta kasar Sifaniya) da Esther Okoronkwo (mai wasa Changchun FC ta kasar China) da Asisat Oshoala (mai wasa a kungiyar Bay FC ta Amurka) da Uchenna Kanu (mai wasa a kungiyar Racing Louisville ta Amurka) da Chiwendu Ihezuo (mai wasa a kungiyar Pachucha Club de Futbol ta kasar Mexico) da kuma Chinonyerem Macleans (mai wasa a kungiyar Locomotiv Moscow ta kasar Rasha).