Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Shirya Gasar Olympic Zata Mikawa Lashinda Demus Lambar Zinariyarta Bayan Shekaru 12


Wannan ne karon farko da za’a gudanar da bikin mika lambobin girmamawar a yayin gasar wasannin Olympic na bazara.

Lashinda Demus ta sanarda cewar Hukumar shirya wasannin Olympic ta Duniya na shirin mika mata lambar zinariya tare da takwarorinta da suka samu lambobin azurfa da tagulla a yayin bikin da zai gudana a ranar 9 ga watan Agusta mai zuwa a dandalin zakaru na birnin Paris dake karkashin hasumiyar Eiffel.

Wannan ne karon farko da za’a gudanar da bikin mika lambobin girmamawar a yayin gasar wasannin Olympic na bazara.

A cewar Demus, “ina zaton suna kokari ne su kwatanta lamurin ya kusan dacewa da zahiri.” Anan ba zan samu damar kwalewar samun nasara a tsere ba, ko tsayawa akan dandamali domin karbar kyauta, ko hira da ‘yan jaridu bayan cin lambar zinariya, da makamantan hakan. Saidai ina ganin sun yi iya bakin kokarinsu, ina kuma yaba musu akan hakan. Hakan zai kwantar min da hankali.”

A maimakon ta mayarwa Hukumar shirya gasar Olympics da lambar azurfar ta gidan waya kamar yadda aka bukata, Demus ta dauki hayar lauyan daya tuntubi wadanda suka samu lambobin azurfa da tagulla, Zuzana Henjnova daga Jamhuriyar Czech da Kaliese Spencer daga Jamaica.

Tare, suka dage har saida hukumar shirya gasar ta amince ta shirya bikin basu lambobin yayin gasar ta birnin Paris.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG