Uwargidan Shugaban Najeriya, Remi Tinubu ta yabi ‘yan wasan Super Falcons bayan da suka samu gurbin zuwa gasar wasannin Olympics da za a yi a Paris.
Rabon da tawagar mata ta Najeriya ta je gasar tun shekaru 16 da suka gabata.
“Kawo karshen rashin zuwa gasar wasannin Olympics da aka kwashe shekaru 16 ba a je ba, ba karamar nasara ba ce.
“Jajircewarku da nuna juriya da yin aiki tare sun sa Najeriya tana mai alfahari tare da kwadaitar da ‘yan mata da babu adadi a sassan kasar nan.” Remi Tinubu ta ce a cikin wata sanarwa da ta fitar a kafafen sada zumunta.
A ranar Talata tawagar ‘yan wasan ta mata karkashin jagoranci mai horarwa Randy Waldrum ta yi nasara akan ‘yan wasan Afirka ta Kudu Bayana-Bayan bayan da aka yi jimullar kwalaye da ci 1-0 a wasanni biyu da suka buga.
A wasan da aka buga a Abuja a makon da ya gabata, Super Falcons ta yi nasara da ci 1-0 yayin da aka tashi canjaras a wasan da suka buga a Pretoria a ranar Talata.
Najeriya tana rukunin 'C' mai dauke da Sifaniya, Japan da Brazil.
Lokaci na karshe da Super Falcons ta je gasar tun wanda aka yi a shekarar 2008 a Beijing.
C
Dandalin Mu Tattauna