Hukumomin Faransa sun fada a jiya Talata cewa masu yawon shakatawa dake niyar zuwa kallon bukin buden wasannin Olympics a Paris ba za su iya yin haka ba, yayin da kasar take shirin ko-ta-kwana sakamakon barazanar tsaro a lokacin wasan.
A jiya Talata ne Ministan harkokin cikin gida na Faransa Gerald Darmanin yace ba a gano takamaiman wata barazana ba, amma akwai yiwuwar fuskantar barazana da dama daga hare haren kungiyoyin ta’addanci da kuma ayyukan kutsen yanar gizo daga Rasha.
Sama da shekaru goma kenan da kungiyoyin ta’addanci ke ta auna Faransa kana a watan Oktoban bara kasar ta kasance cikin cikakken shirin ko-ta-kwana kan hare haren ta’addanci bayan da ake zaton wani dan ta’adda ya shiga wata makaranta kana ya cakawa wani malami wuka.
A makon da ya gabata ne, wani mutum ya sace shirin dabarun tsaro da aka yiwa wasan Olympic a Paris daga wani ma’aikaci.
Tun lokaci ne kuma aka daure wanda ya yi satar kana Faransa ta kasance cikin shirin tinkarar sauran barazana.
Dandalin Mu Tattauna