Bankin duniya ya amince ya bai wa jamhuriyar Nijer tallafin billion 214 na kudaden CFA kuma kwatankwacin dalar Amurka miliyan 350 domin karfafa aiyukan noma da kiwo .
Wannan na zuwa a wani lokacin da farashin kayan abinci ke ci gaba da tashin gauron zabi saboda haka ake ganin bunkasa wadanan fannoni, mataki ne da ka iya taimakawa a sami wadatar abinci har ma a kai matsayin da za a iya sayarwa don samar da kudaden shiga ga al’ummar kasar.
Shugaban kungiyar manoma da makiyaya ta Plateforme Paysanne, Djibo Bagna, ya yaba da wannan yunkuri da ka iya zama hanyar warware matsalar karancin abinci da tsadarsa a Nijar.
Ya kuma bada wasu shawarwarin da yake ganin zasu taimaka a cimma nasarar abinda aka sa gaba a kasar da ke daya daga cikin mafi dandana kudar illolin canjin yanayi a duniya.
Abdou Nino Gajango daya daga cikin jagororin masu aiyukan ci gaban karkara na da kwarin gwiwa game da fa’idar wannan dabara amma fa yace sai an cire son rai wajen zartar da abubuwan da aka tsara.
Kashi 40 cikin 100 na kudaden shiga a Jamhuriyar Nijar kan fitowa ne daga aiyukan noma inji Bankin Duniya wanda ya kara da cewa fannin na zama madogara ga kashi 80 cikin 100 na yawan al’ummar kasar.
Bankin ya kara da cewa abunda ya sa aka dauki matakan inganta kasuwannin sayar da albarkatun noma da kiwo ta hanyar wannan tallafi.
A yanzu haka farashin abinci ya yi tsadar da ba a taba ganin irinta ba a tarihin Nijar. La’akari da girman wannan matsalar ya sa gwamnatin mulkin sojan kasar bullo da tsarin sayar da shinkafa a farashi mai rangwame a birnin Yamai shirin da aka ayyana cewa za a fadada shi zuwa jihohi a nan gaba.
Idan ba a manta ba, Bankin Duniya ya dakatar da aiyukansa a Nijar a washegarin juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023 kafin ya sanar cewa ya dawo aiki a watan Mayun da ya shige.
Saurari rahoton Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5