Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wutar Lantarki: Najeriya Ta Samu Lamunin Dala Miliyan 500 Daga Bankin Duniya


Bankin Duniya
Bankin Duniya

Najeriya ta samu lamunin dala miliyan 500 da bankin duniya ya baiwa bangarenta na wutar lantarki domin bunkasa rarraba wutar ta lantarki.

WASHINGTON, D. C. - Lamunin na zuwa ne bayan da aka yi karin kudi a watan da ya gabata ga manyan masu amfani da wutar ta lantarki, a kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a Afirka.

Hukumar da ke kula da kasuwancin gwamnati (BPE) mai kula da harkokin kasuwanci a kasar a ranar Alhamis ta ce bankin duniya ne ya amince da rancen a shekarar 2021 kuma ya hada da shirin karbar rancen gwamnati a wannan wata bayan cimma wasu nasarori.

Wannan lamuni na rangwamen na da nufin inganta harkokin kudi da fasaha na kamfanonin rarraba wutar lantarki, wadanda ke kokarin kara karfin aiki fiye da shekaru goma bayan da Najeriya ta mika wa kamfanoni masu zaman kansu bangaren wutar lantarki.

A watan da ya gabata ne hukumar kula da wutar lantarki ta kara haraji ga masu amfani da wutar lantarki, da ke amfani da wutar mafi yawa a Najeriya a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke da niyyar cire tallafin tattalin arziki domin rage matsin lamba ga kudaden gwamnati.

A baya dai Bankin Duniya ya ba da shawarar rage tallafin da Najeriya ke bayarwa wajen inganta harkokin kudaden gwamnati.

Bangaren wutar lantarki a Najeriya na fuskantar matsaloli da dama da suka hada da gazawar wutar lantarki, karancin iskar gas, bashi da kuma barna.

Kasar dai na da megawatts 12,500 da aka girka amma kusan kashi daya bisa hudu ne ke samar da wutar lantarki, lamarin da ya sa ‘yan Najeriya da dama ke dogaro da injinan dizal masu tsada.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG