Najeriya ta bukaci tsawaita wa'adin shirin bada tallafin bankin duniya na rancen dala miliyan 800 da watanni 18 domin inganta shirye-shiryenta na baiwa al'umma kariya.
Bukatar na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalolin hauhawar farashi da kalubalen tattalin arziki.
A cewar wani kundin sauya fasalin aikin na Bankin Duniyan, gwamnatin Najeriya ta bukaci a tsawaita wa'adin kawo karshen aikin daga ranar 30 ga watan Yunin da muke ciki, zuwa 31 ga watan Disamban badi.
A cewar rahoton, kimanin magidanta masu karamin karfi milyan 3 suka ci gajiyar shirin tallafin rancen dala milyan 800.
Babban Bankin Najeriya ya rarraba rancen domin rage radadin manufofin gwamnati na baya-bayan nan, irinsu janye tallafin man fetur.
Daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin, magidanta dubu 700 sun fito ne daga yankunan karkara kuma kimanin magidanta milyan 2 da rabi sun fito ne daga birane.
Tsawaita wa'adin na neman a sake tsara wa'adin gudanar da aikin tare da inganta shirin gwamnatin najeriya na tallafawa al'umma, inda ya kara da cewar mazauna birni dubu 1 da 652 aka shigar cikin shirin ta hanyar tsarin zakulowa da shirin ya bullo da shi.
Dandalin Mu Tattauna