Sanarwar ta ce wannan lamuni zai taimaka wajen kara bunkasa sashen hada-hadar kudi na Ghana bayan shirin gwamnati na musanya bashin cikin gida (DDEP) ya shafi wasu cibiyoyin hada-hadar kudi a kasar.
Masani kan harkokin kudi da tattalin arziki, Hamza Attijany da yake karin bayani kan wannan bashi yace, “Wannan bashi ne da gwamnati ta nema domin magance wasu matsaloli da bankuna da wasu cibiyoyin kudi na kasar ke fuskanta bayan musayar bashi tsakaninsu da gwamnati.
"Hakan ya addabi wasu bankuna da cibiyoyin kudi har ba su iya tafiyar da harkokinsu yadda ya kamata. Domin haka gwamnati ta bukaci wannan bashi don ta taimaka musu tafiyar da harkokinsu”, in ji shi.
Daraktan Bankin Duniya na Ghana, Laberiya, da Saliyo Robert R. Talierco, yace, wannan bashin zai taimakawa Ghana da masu hada-hadar kudi, kuma “zai amfanar da bangaren hada-hadar kudi da tattalin arzikin Ghana ta hanyar tallafawa masu ajiya da sauran masu amfani da kudi da tanadi”.
Sai dai masani kuma mai sharhi kan tattalin arziki, Sarki Imrana Hashiru Dikeni yace, wannan bashi zai taimaka ne na dan gajeren lokaci, idan aka yi la’akari da matsalolin kudi da kasar ke fuskanta. Yace, biyan wannan bashi zai yi wuya domin ba kasuwanci za a yi da kudin ba, za a zuba su ne inda ba za su haifar da riba ba.
Wasu ‘yan Ghana sun bayyana mabanbantan ra’ayi game da amfani da bashin inda ya dace inda su ka ce, mai yiwuwa gwamnati ta zuba kudaden inda bai dace ba, musamman ma yanzu da yake babban zabe na karatowa.
Wasu kuma suka ce, idan gwamnati ta taimakawa cibiyoyin hada-hadar kudi, za su baiwa ‘yan kasa rance don bunkasa sana’o'insu, kuma hakan zai kara bunkasa tattalin arziki.
Kungiyar raya kasa da kasa IDA dake karkashin bankin duniya, na daya daga cikin manyan hanyoyin samun taimako ga kasashe 74 mafi talauci a duniya, wadda 39 daga cikinsu na nahiyar Afirka.
Saurari rahoton Idris Abdullah:
Dandalin Mu Tattauna