Firai Ministan ya kara da cewa, ta yiwu Isra'ila zata tura sojojinta zuwa bakin iyakar kasar da Lebanon, inda dakarun kasar ke fafatawa da ‘yan kungiyar Hezbullah na Lebanon a duk rana.
Fada tsakanin Isra'ila da kungiyar Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran ya zafafa a 'yan makonnin da suka gabata, abinda ke kara kawo fargabar yiwuwar barkewar rikici a yankin.
A wata hira da yayi da gidan talabijin din Isra'ila na Channel 14, Netanyahu ya ce tura sojojin zuwa arewacin iyakar kasar zai karfafa tsaron kasar don tunkarar kungiyar Hezbollah, matakin zai kuma ba Isra'ilawan da suka tserewa fadan a kusa da iyakar Lebanon damar komawa gidajensu.
Ya kara da cewa yayin da yake fatan a lalubo hanyar warware rikicin da kungiyar Hezbollah ta hanyar diflomasiyya, Isra'ila na iya "yaki ta bangarori da yawa, kuma ma suna kan shiri.
Shugaban Amurka Joe Biden ya jinkirta samar da manyan bama-bamai tun cikin watan Mayu saboda damuwar kan kai hari da Isra'ila ke ci gaba da kai wa a Gaza, sai dai a makon da ya gabata gwamnatinsa ta musanta zargin da Netanyahu n ya yi cewa, dakatar da tura makaman ya shafi sufurin wasu kayayyaki.
Ku Duba Wannan Ma Macron Ya Fusata Da Harin Da Isra'ila Ta Kai A Rafah