Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Kiran Kada Kuri'a A MDD Game Da Tsagaita Wuta A Gaza


Jor Biden Da Banjamin Netanyahu
Jor Biden Da Banjamin Netanyahu

Ana kyautata zaton cewa sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken zai gana da shugabanni a Misra da Isra'ila yau Litinin da zumar cimma nasarar dakatar da fadan.

Amurka tayi kira da a kada kuri'a akan daftarin matsayar kwamitin tsaron Majilisar Dinkin Duniya wanda ya bukaci Hamas ta amince da sharudan da aka gindaya mata na yarjejeniyar tsagaita wuta, yayın da ake kyautata zaton cewa sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken zai gana da shugabanni a Misra da Isra'ila yau Litinin da zumar cimma nasarar dakatar da fadan.

Da farko, Blinkin zai gana da shugaban kasar Masar Abdel Fattah El-Sısı a Cairo sannan daga bisani zai gana da Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ministan tsaro, Yoav Gallant.

Ziyarar ta babban jami'in diflomasiyyar Amurka za ta kai shi Qatar da Jordan, inda zai hallarci wani taro inda za a tattauna akan agajın jin kai a Gaza.

Jami'an Amurka sun ce Isra'ila zata amince da sharuddan da aka gindaya mata wanda ya hada da dakatar da fada, sako wasu daga cikin mutanen da ake garkuwa da su a Gaza, sako wasu fursunoni ‘yan Filasdinu da Isra’ila take tsare da su, karin agajin jinkai ga Falasdinawa, janyewar dakarun Isra’ila daga yankunan da mutane suke zaune a Gaza da kuma dawowar Falasdinawa fararen hula zuwa gidajensu.

Yakin Gaza ya biyo bayan harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 1,200 a Isra'ila, galibi fararen hula, a cewar alkaluman hukuma na Isra'ila, inda suka kuma yi garkuwa da kusan mutane 250.

Martanin sojan Isra'ila ya kashe Falasdinawa sama da 37,000, galibi mata da yara, a cewar ma'aikatar lafiya ta Gaza.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG