Shugaban Kasa Bola Tinubu yayi allawadai da hare-haren baya-bayan nan da aka kaiwa al’ummomin kananan hukumomin dutsin-na da kankara a jihar Katsina.
Da yake bayyana hare-haren baya-bayan nan da masu matukar muni, shugaban kasar ya jaddada cewar za’a dauki karin matakai wajen tabbatar da tsaron al’umma tare da ganin bayan ‘yan ta’adda da sauran ‘yan ina da kisa a ko’ina a fadin Najeriya.
Sanarwar da hadimin shugaban kasar na musamman akan harkokin yada labarai, Ajuri Ngilale, ya fitar a yau Talata tace, Shugaba Tinubu ya baiwa hukumomin tsaro umarnin farauto wadanda suka kai hare-haren tare da gurfanar dasu a gaban kuliya.
Shugaban kasar ya kuma mika sakon ta’aziyarsa ga iyalan mamatan, dama gwamnati da al’ummar jihar katsina, sa’annaa yayi addu’ar neman gafara ga rayukan wadanda suka mutu.
Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da ‘yan bindiga dauke da muggan makamai suka afkawa kauyen Gidan Boka, tare da hallaka mutane 20 da jikkata wasu mutum 2.
Jami’an tsaron da ‘yan ta’addar suka hallaka sun hada da jami’an ‘yan sanda masu mukamin sufeta 3 da kofur daya da kuma askarawan tsaron gwamnatin Katsina 2.