Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Kankara: Gwamna Radda Ya Sha Alwashin Samun Galaba Akan ‘Yan Bindiga


Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda

A yau Talata, Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda, ya sha alwashin samun galaba a yakin da yake yi da matsalar ‘yan bindiga sakamakon harin baya-bayan nan da suka kai kan mutanen da basu ji ba basu gani ba a kauyen Gidan Boka dake karamar hukumar Kankara ta jihar.

Al’amarin, wanda ya faru a Lahadin data gabata, 9 ga watan Yunin da muke ciki, da misalin karfe 3 na rana, yayi sanadiyar mutuwar mutane 26, ciki harda askarawan tsaron gwamnatin Katsina 2, da jami’an ‘yan sanda 4 da mazauna kauyen 20, sa’annan an jikkata wasu mazauna kauyen 2.

Da yake mika sakon ta’aziyarsa ga iyalai da dangin mutanen da al’amarin ya rutsa dasu, gwamnan ya bi sahun sauran al’ummar jihar Katsina wajen gudanar da addu’o’in neman gafara ga rayukan wadanda suka mutu tare da jajantawa iyalansu game da mummunan yanayin da suka tsinci kansu a ciki.

Sanarwar da Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Katsina, Ibrahim Kaula, ya fitar tace, harin da ‘yan bindigar suka kaddamar a Lahadin data gabata, a janyo koma baya ga kokarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya da tsaron al’ummar jihar.

Gwamnan ya kuma yabawa kokarin da hukumomin tsaro suke yi na tunkarar ‘yan bindigar dake barazana ga zaman lafiya a jihar, inda yace, gwamnatinsa zata cigaba da jajircewa a kokarin kawar da ayyukan ‘yan bindiga da dukkanin nau’ukan laifuffuka a jihar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG