Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Laraba A Matsayin Ranar Hutun Dimokradiyya

Ministan Cikin Gida, Olubunmi Olatunji-Ojo
Ministan Cikin Gida, Olubunmi Olatunji-Ojo

A sanarwar daya fitar a yau Talata, Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, wanda yayi ayyanawar a madadin gwamnatin tarayya, ya taya ‘yan Najeriya murnar zagayowar ranar.

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 12 ga watan Yunin da muke ciki ta zamo ranar hutun bikin zagayowar ranar dimokradiyya.

A sanarwar daya fitar a yau Talata, Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, wanda yayi ayyanawar a madadin gwamnatin tarayya, ya taya ‘yan Najeriya murnar zagayowar ranar.

Tunji-Ojo ya ce, "Yayin da muke sake bikin ranar dimokuradiyya a cikin tarihin kasarmu mai daraja, mu tuna ƙokarin iyayenmu da suka yi kuma mu tabbatar da cewa Najeriya ta ci gaba da kasancewa kasa daya, amintacciyar kasa da samun zaman lafiya da rashin rabuwan kawuna."

Ministan ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya dama kawayen kasar dasu yabawa irin cigaban da aka samu tare da sa ran samun kyakkyawar makoma ga dimokiradiyar Najeriya.

A shekarar 2018, shugaban kasar wancan lokaci, Muhammadu Buhari ya sauya ranar dimokiradiya daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni domin karrama daya daga cikin gwarazan dimokiradiyar kasar, Cif M.K.O Abiola.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG