Kungiyar Rivers Hoopers ta kafa tarihi a Litinin din data gabata a filin wasa na birnin Kigali inda suka yi galaba akan tsaffin zakarun kwallon kwando na Amurka “Monastir”inda suka tsallaka zuwa zagayen kusa dana karshe.
Kungiyar kwallon kwandon Najeriya ta farko data samu nasarar tsallakawa zuwa zagayen kusa dana karshe a gasar ta nahiyar Afrika ta lallasa zakarun kasar Tunisia da ci 92 da 88.
Kungiyar dake karkashin jagorancin mai horaswa Ogah Odaudu sun yi namijin kokari, inda suka mamaye wasan tare da yin duk mai yiyuwa. A karshe suka kafa tarihi.
A karshe dai kungiar Al-Ahly ta kasar Libya tayi galaba akan Rivers Hoopers a jiya Laraba 29 ga watan Mayun da muke ban kwana da shi a wasan kusa dana karshen, yanzu kuma zata tunkari kungiyar Cape Town Tigers a gobe Juma’a, 31 ga watan na Mayun.