Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Giannis Antetokounmpo Zai Je Najeriya Karon Farko


Giannis Antetokounmpo
Giannis Antetokounmpo

Giannis Antetokounmpo shahararran ‘dan wasan kwallon kwando ya lashe lambar yabo ta NBA MVP guda biyu da gasar NBA guda daya. An zabe shi zuwa gasar shahararrun ‘yan wasa kwando karon farko, sau biyar kuma ya buga wasanni bakwai a cikin wasan na fitattun 'yan wasa.

WASHINGTON, D. C. - Ya fara nuna hazaka tun yana matashi da ya girma a kasar Girka inda ya zama daya daga cikin manyan ‘ƴan wasan kwallon kwando na musamman, ‘dan wasan gaba mai tsawon kafa 6'11 wanda ya ke dokewa, da razana abokan hamayyarsa da irin wasansa mai karfin iko a filin wasa, da ya hada da irin sifarsa kosasshe mai koshin lafiyaya da kuma karfin gaske.

Giannis Antetokounmpo
Giannis Antetokounmpo

Ya yi abubuwa da yawa, amma bai taba zuwa kasar mahaifansa ta Najeriya ba sai yanzu. Wani sabon shirin mai suna Ugo, labarin sa ne na zuwa gida da aka yi tare da hadin gwiwar WhatsApp, ya ba da haske game da tafiya Giannis ta farko zuwa Najeriya, tare da mahaifiyarsa da ta yi hijira daga Najeriya zuwa kasar Greece kusan shekaru arba'in da suka gabata.

A cikin fim din mai tsawon mintuna 31 wanda Rick Famuyiwa ya jagoranta, Giannis ya tsunduma cikin al'adun danginsa da al'adun Najeriya, yana gano tushensa da jimame a zuciyarsa.

Giannis Antetokounmpo
Giannis Antetokounmpo

"Na girma a Greece, al'adata ta Najeriya abu ne da mahaifiyata ta tabbatar da cewa yana tare da mu, amma ban taba yin sa'ar samun zuwa kai tsaye kasar Najeriya ba," in ji Giannis. "

Samun damar komawa inda aka haifi mahaifiya ta, da sake samun wani sabon iyali a Najeriya, ya kasance daya daga cikin abubuwan da suka fi dacewa a rayuwata, kuma hakan ya sa na ƙara alfahari da yawancin al'adu da suka sa ni zama yadda nake. Ina alfaharin nunawa duniya labarin wannan tafiya, don nuna wa mutane, na kuma nuna mana cewa dukanmu muna da wurin da muke dauka ‘gida’, ko da kuwa muna zaune a nesa.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG