Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasannin Gasar Kwallon Kwando Ta Afirka BAL


Tambarin Gasar Wasannin BAL
Tambarin Gasar Wasannin BAL

Yayin da gasar Kwallon Kwando ta Afirka (BAL) ta shiga zango na uku, muna dauke da dukkan bayanan da ake bukatar sani a kakar wasan ta bana.

Tun ranar 11 ga watan Maris aka bude babbar gasar kwallon Kwando ta Afirka, inda fitattun kungiyoyin wasan kwallon Kwando na Afirka 12 ke karawa da juna a kasashen Senegal da Masar da kuma Rwanda.

An rarraba kunyiyoin rukuni biyu, rukunin Sahara da rukunin Nile, kowanne rukunin na dauke da kungiyoyin wasa shida da zasu kara da juna har sai an sami zakara a kowanne rukuni.

Kungiyoyin da ke rukunin Sahara za su buga wasansu daga ranar 11 ga watan Maris zuwa 12 a birnin Dakar. Sai kuma rukunin Nile da zai gudanar da wasanninsa a filin wasan Moustafa dake birnin Alkahira daga ranar 26 ga watan Afrilu zuwa 6 ga watan Mayu.

Kungiyoyi hudu ne daga kowanne rukuni za su sami damar fafatawa a wasannin karshe na gasar BAL wadanda cikinsu ne za a sami kungiyar da za ta kasance zakarar wasan bana, wadda za a yi a kasar Rwanda daga ranar 21 zuwa 27 na watan Mayu.

Kungiyoyi biyar da suka fara buga wasanninsu na farko daga rukunin Sahara da sun hada da ABC Figthers ta kasar Ivory Coast da AS Douanes na kasar Senegal da Kwara Falcons na Najeriya da kungiyar REG ta kasar Rwanda, sai kungiyar Stade Malien ta Mali da kuma US Monastir da kasar Tunisiya.

A bangare na biyu na gasar na rukunin Nile wanda kunyiyoyin wasan suka hada da Al Ahly daga Masar, sai Cape Town Tigers daga kasar Afirka ta Kudu, da CFV Beira ta Mozambique, da kuma Petro de Luanda daga Angola, da SLAC daga kasar Guinea.

Muryar Amurka ta kasance babbar abokiyar watsa shirye-shiryen gasar BAL ta Afirka, kuma za ta ci gaba da watsa wasannin ta kafar radiyo cikin rayuwa daban-daban.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG