Al’ummar Chikun Sun Yi Zanga-Zanga Akan Harin ‘Yan Bindiga A Kaduna

Cunkoson ababen hawa akan hanyar Kaduna zuwa Abuja

Al’ummar Garin Goningora dake karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna sun tare babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja sakamakon harin da ‘yan bindiga suke kaiwa yankin.

A yayin harin da aka kai a daren Larabar data gabata, an samu rahoton sace dimbin al’ummar yankin tare da raunata wasu da dama.

Da safiyar Alhamis din nan ne wasu fusatattun mazauna yankin, suka rufe babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Al’amarin dai ya sabbaba cunkoson ababen hawa akan hanyar, inda masu motoci da matafiya suka makale.

An bada rahoton mutuwar mutane 2 ciki har da wani mamba na dakarun tsaron farin kaya na Civilian Jtf yayin harin.

Harin baya-baya nan akan al’ummar Goningora na zuwa ne mako guda kacal bayan da sojoji suka hallaka wani rikakken me garkuwa da mutane me suna Boderi Isyaku, tare da wasu mayakansa a karamar hukumar ta Chikun.

Ku Duba Wannan Ma Gwamnatin Kaduna Ta Tabbatar Da Kashe Boderi Isyaku, Dan-Fashin Dajin Da Ya Addabi Jihohin Arewa

Haka kuma, an ce ‘yan bindigar sun cinnawa wata motar sulke ta soja wuta sa’ilin da sojoji suka yi yunkurin dakile harin.

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida a jihar Kaduna, Samuel Aruwan da jami'in tsaro

Saida gamayyar jami’an tsaro karkashin jagorancin Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Kaduna da Kwamishinan ‘Yan Sanda da Daraktan Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS na jihar suka halarci wurin da zanga-zangar ke gudana tare da rokon fusatattun al’ummar yankin su bude hanyar domin baiwa ababen hawa damar wucewa tare da bada tabbacin cewar ana kokarin kamo ‘yan bindigar da kubutar da mutanen da suka sace.

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida a jihar Kaduna, Samuel Aruwan da jami'in tsaro a kan hanyar Kaduna Zuwa Abuja