Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Chadi Ta Sanar Da Ranar Zabe Don Komawa Tafarkin Dimokradiyya


Shugaban kasar Chadi Idriss Mahamat Deby.
Shugaban kasar Chadi Idriss Mahamat Deby.

Hukumar zaben kasar Chadi ta ba da sanarwar ba zato a ranar Talata cewa, za a gudanar da zaben shugaban kasa wanda zai kawo karshen mulkin soji na tsawon shekaru uku a yankin tsakiyar Afirka a ranar 6 ga watan Mayu.

Hukumar zabe ta kasar Chadi ta ce za a gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 6 ga watan Mayu. Ta ce zabukan za su dawo kan tsarin tafarkin mulkin dimokaradiyyar kasar, kuma za su kawo karshen wa'adin mulkin Janar Mahamat Idriss Deby, wanda yanzu ya cika shekara ta uku.

Mahamat mai shekaru 37 ya zama shugaban kwamitin rikon kwarya na sojojin Chadi a watan Afrilun 2021 bayan mutuwar mahaifinsa, Idriss Deby Itno, a lokacin da yake yakar 'yan tawayen arewacin kasar. 'Yan tawayen dai sun ce suna son kawo karshen mulkin Deby na tsawon shekaru 31.

Shugaban ya karbi mulki daga hannun mahaifinsa kuma ya yi alkawarin jagorantar majalisar rikon kwarya ta watanni 18, amma a watan Oktoban 2022 ya rusa majalisar tare da ayyana kansa a matsayin shugaban rikon kwarya.

Har yanzu dai ba a san ko ‘yan takara nawa ne za su fafata a zaben na ranar 6 ga watan Mayu ba. Sai dai a watan da ya gabata, tsohuwar jam'iyyar Patriotic Salvation Movement ko MPS mai mulki a Chadi ta ce Mahamat Idriss Deby ne zai zama dan takarar jam'iyyar.

Wasu gungun 'yan adawar kasar Chadi sun gana a ranar litinin, kwana guda gabannin bayyana ranar zaben, domin zabar dan takararsu. Su ma sun yanke shawarar marawa shugaba Deby baya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG