Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gurfanar Da Sojoji 17 Da Ake Zargi Da Aikata Laifuka Daban-Daban A Gaban Kotun Sojin Najeriya


Kotun Soja Ta Musamman Da Ke Jos, Jihar Filaton Najeriya
Kotun Soja Ta Musamman Da Ke Jos, Jihar Filaton Najeriya

Shelkwatar rundunar sojin Najeriya da ke Jos, jihar Filato ta gurfanar da wasu jami'anta goma sha bakwai a gaban wata kotu ta musamman, bisa zarginsu da aikata laifukan da suka sabawa tsarin aikinsu.

Wadanda aka gurfanar a gaban Kotun Sojin, da suka hada da wani jami'i mai babban mukami daya, da sauran sojoji goma sha shida da ake zarginsu da aikata kisa, safarar makamai da sauran manyan laifuka.

Da yake kaddamar da kotun a Shelkwatar rundunar ta uku, Maxwell Khobe da ke Jos, Shugaban kotun sojin, Birgediya Janar Liafis Bello ya jaddada muhimmancin yin da'a, biyayya da tsarin mulki da kwarewar aiki a tsakanin sojin Najeriya.

Birgediya Janar Bello ya ce kotun za ta yi adalci wajen tabbatar da cewa dukkan masu ruwa da tsaki sun bi ka'ida wajen yin hukunci da adalci ga kowa.

Kotun Soji Ta Musamman Da Ke Jos, Jihar Filaton Najeriya
Kotun Soji Ta Musamman Da Ke Jos, Jihar Filaton Najeriya

Shugaban kungiyar dake samar da adalci wa bil'adam mai suna YIAVA, Kwamared Pwakim Jacob Choji ya ce tun can al'umma na kokawa da ayyukan wasu gurbatattun jami'an tsaro.

Shima Shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah a karamar hukumar Mangu, Yahaya Bello Shanono ya ce sun yaba da matakin gurfanar da sojojin a gaban kotu.

Tun farko alkalin kotun sojin, Manjo Janar Nasir Abdullahi, ya ce gurfanar da wadanda ake zargin na nuni da cewa runduna ta uku ba da wasa take yi ba, wajen yin adalci ba tare da la'akari da matsayin jami'i ba.

Court Marshall in Jos, Plateau State, Nigeria
Court Marshall in Jos, Plateau State, Nigeria

Kotun ta dage sauraron kararrakin zuwa ranar shida ga watan Maris mai zuwa.

A halin da ake ciki kuma, rundunar sojin ta uku da ke Jos, ta karrama wasu jami'anta su takwas, bayan sun ki amincewa da karbar rashawa na Naira miliyan daya da dubu dari biyar daga hannun wasu barayin shanu.

Barayin sun sato shanu guda talatin ne na wani mai suna Shehu Umar da ke garin Mangu.

Jami'an sojin takwas sun ki karbar na goron suka kuma damke barayin.

Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG