Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Masallata A Wani Masallaci A Zamfara


Yan bindiga
Yan bindiga

‘Yan bindiga sun sace dimbin masallata a daya daga cikin masallatan garin Tsafe, Shelkwatar Karamar Hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Kafafen yada labaran jihar Zamfara sun bada rahoton cewar ‘yan bindigar, wadanda suka yo zuga, sun mamaye masallacin ne da misalin karfe 5 na assalatu sa’ilin da mutanen ke daf da tada sallar asubahi.

An ruwaito cewar ‘yan bindigar sun ajiye baburan su ne nesa da masallacin domin kada masallatan su ankara da zuwansu.

A cewar wani ganau, adadin masallatan da aka sace na iya haura mutum 30.

Haka shima, wani shugaban al’umma, wanda aka tattauna da shi ta wayar tarho da kuma ya nemi a sakaya sunansa, yace askarawan tsaron al’umma sun bi sawun ‘yan bindigar da nufin kubutar da masallatan da aka sace.

Duk kokarin jin ta bakin me magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, asp Yazid Abubakar ya ci tura, kasancewar an yi ta buga wayarsa bata shiga.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG