Jam'iyyu a Najeriya na shirin karshe na mika sunayen 'yan takarar shugaban kasa ga hukumar zabe ta INEC, yayin da Atiku Abubakar na PDP ya tabbatar da zabar gwamnan Delta Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakinsa a takara.
Hakan na faruwa a jajiberin ranar rufe mika sunayen gwanaye.
Hukumar zabe ta ce manhajar tara sunayen za ta rufe kirib a ranar Jumma’ar nan 17 ga watan nan na Yuni.
Manyan jam’iyyu na bin kowace irin dabara wajen cankar dan takarar mataimakin shugaban kasa da zai jawo mu su tagomashin lashe zabe, don haka sai da a ka yamutsa gashin baki kafin cankar Okowa maimakon gwamnan Ribas Nyesom Wike.
Atiku ya fara tabbatar da wannan zaben a shafinsa na yanar gizo inda helkwatar PDP ke jan kafa wajen bayyana sunan.
A APC kuma da lamarin ya fi daukar hankali, har yanzu ana kan tantance sunaye ne.
Shi kuma ma"ajin NNPP Shehu Barau Ningi na cewa matukar su ka samu mataimakin dan takara ga Kwankwaso mai tasiri za su iya lashe zabe.
Kawo la'akari da bambancin addini ga 'yan takarar na haddasa tsaiko wajen tsayar da mataimaka duk da hakan ba tanadin tsarin mulki ba ne.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El Hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5