Yanzu dai za a iya cewa tsohon mataimakin Shugaba kasa Alhaji Atiku Abubukar na jamiyar PDP, ya yi nasa nazarin na wanda zai yi masa takaran mataimakin shugabancin kasan, na neman kuri'u a wasu sassan Najeriya, yayin da Bola Ahmed Tinubu dan takaran jam'iyar APC shima ke fustantar makamancin hakkan.
Dukkan 'yan takarar manyan jam'iyun siyasar sun fito daga shiyoyi daban daban, yayinda kuma suka kasance mutane masu karfin gaske ta fannin siyasa wanda ake ganin cewa wannan shine irin siyasar da za a yi ta na farko, da za su bukaci dauko dauko mutum mai kafi a siyasance kafin su samu kuri'un wannan shiya.
Yanzu dai wadannan 'yan takara na zawarcin jami'iyun adawa, don samun kuri'u daga wannan shiya da zai kai su ga nasara a zaben 2023.
Koda shike dukan jam'iyun biyu na fuskantar korafe korafe a wajen magoya bayansu inda wasu suka nuna kin amicewarsu, yayinda wasu daga cikinsu suka fice suka bar jam'iyun.
Da alamu wasu jam'iyun ba kasafe ake jin muryansu ba dan rashin masu gida rana wanda ko a wajen yakin neman zaben, ba su samu zagawa wasu jahohin ba.
Rahotanni na nuni da cewa, ana wata turka turka tsakanin 'yayan jam'iyar APC, wato a tsakanin mutun na uku a taraiyar Najeriya kuma shugaban majalisar Dattawa, Sen Ahmed Lawan da Alh Bashir Machinama wanda ya lashe zaben fidda gwani domin tsayawa takarar sanata a mazabar shugaban majalisar dattawan bayanda shugaban majalisar dattawan ya fadi zabe ya dawo yana nema ya maye gurbin Machinama da aka zaba. Tayin da Machinama ya ce a kai kasuwa.
Bisa bayanai da suka fito, na nuna da cewa, Saneta Ahamed Lawan ya saya tikitin na tsayawa takaran Shugabancen kasa da kuma dan majalisar dattawa kana ya mika wa Alh Machinamana tikitin tsayawa takarar majisar, kamar yadda wasu 'yan siyasa ke yi. Amma daga bisani, bayan da ya fadi zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa, ya nemi karbar gurbin takarar kujeararsa sai dai Alh Machinamana yace "ba da shi ba gada a kotu" don kuwa shi ya lashe zaben fid da gwani na jam'iyyar APC.
Bayanai na nuni da cewa, mutane biyu, da gwannan jahar Yobe da wasu jijaga jigan jam'iyar suna ta gudanar da tararuka daban daban don warware wannan matsalan.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: