Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP Ta Kafa Kwamitin Da Zai Tantance Dan Takarar Mukamin Mataimakin Shugaban Kasa

Wani taron PDP da ta yi a baya (Instagram/PDP) an yi amfani da wannan hoto don nuna misali
Wani taron PDP da ta yi a baya (Instagram/PDP) an yi amfani da wannan hoto don nuna misali

Hukumar zabe ta INEC ta bai wa dukkan jam’iyyun siyasar kasar nan da ranar 17 ga watan Yuni, a matsayin wa’adi da za su gabatar da dukkan ‘yan takararsu na mukamai daban-daban da mataimakansu.

Babbar Jam’iyyar adawa ta Peoples’ Democratic Party (PDP) a Najeriya, ta kafa wani kwamiti da zai tantance wanda zai tsayawa jam’iyyar takarar mukamin mataimakin shugaban kasa.

A ranar Alhamis kwamaitin mai mambobi 11, zai fara aikin tantancewar don fitar da wanda zai zama wa Atiku Abubakar abokin takara.

Jam’iyyar ta tsayar da Abubakar, a matsayin dan takarar shugaban kasar jam’iyyar tun makonni biyu da suka gabata.

Wata sanarwa dauke da sa hannun Sakataren kasa na jam’iyyar, Debo Ologunagba, wacce aka wallafa a shafin Facebook din jam’iyyar, ta ce Chief Tom Ikimi ne shugaban kwamitin.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Capt. Idris I. Wada mai ritaya, Chief Osita Chidoka, Binta Bello, Chief Mrs. Alh. Mutiat Adedoja, Austin Opara, da Prof. Aisha Madawaki.

Kwamitin har ila yau na dauke da Mrs. Ayotunde George-Ologun, Chief Mrs. Chidiebelu Mofus, Fidelis Tapgun da kuma Dr. Akilu Indabawa, wanda shi ne sakataren kwamitin.

“Za a fara aikin tantancewar ne a dakin taron kwamitin gudanarwa da ke sakatariyar PDP a Wadata Plaza a Abuja a ranar 16 Yuni, 2022 da misalin karfe 10 na safe.” Kamar yadda sanarwar ta nuna.

Hukumar zabe ta INEC ta bai wa dukkan jam’iyyun siyasar kasar nan da ranar 17 ga watan Yuni, a matsayin wa’adi da za su gabatar da dukkan ‘yan takararsu na mukamai daban-daban da mataimakansu.

XS
SM
MD
LG