Jami’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta tsaida Ahmed Bola Tinubu a matsayin dan takararta na shugaban kasa, yanzu kuma ta na laluben wanda zai kasance mataimakinsa.
An ga hotuna a kafafen sada zumunta dauke da hoton Bola Tinubu da gwamnan jihar Filato Simon Lalong, lamarin da wasu matasa daga shiyyar Arewa ta tsakiya a Najeriya ke ganin ya dace a bai wa Simon Lalong kujerar mataimakin shugaban kasa.
Honarabul Nanlong Nicholas, ya ce shiyyar Arewa ta tsakiyar Najeriya ta cancanci ta sami kujerar mataimakin shugaban kasa saboda aikin wanzar da zaman lafiya da ya yi a jiharsa.
Shi ma John Joshua mazaunin jihar Filato ya ce kasancewar Simon Lalong a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin arewa, zai ba shi damar fahimtar yadda zai iya gudanar da mulkin Najeriya a matsayin mataimakin shugaban kasa.
A gefe guda kuwa, Tsohon karamin Ministan Sadarwa a Najeriya, Ibrahim Dasuki Nakande, ya ce bai kamata a rika sanya addini da bangaranci a batun wanda ya cancanci zama mataimakin shugaban kasa ba.
Jakadan zaman lafiya, Imam Abdullahi Abubakar, wanda a shekarun baya ya tserar da mutane fiye da dari uku daga harin ‘yan bindiga a garin Yalwan jihar Filato, ya ce wanda ya iya hada kan jama’a aka sami zaman lafiya tsakanin mabambantan addinai da kabilu zai iya rike matsayin mataimakin shugaban kasa.
Bayanai dai na nuni da cewa ta yiwu zuwa ranar Laraba jami’iyyar APC za ta sanar da wanda ta zaba a matsayin mataimakin shugaba kasa.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji.