Hukumar EFCC A Najeriya Ta Kama Wasu Matasa 15

Jami’an hukumar dake yaki masu yima tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya ta ‘EFCC’ reshen jihar Lagos, ta kama wasu matasa 15, da ake zargi da aikata zamba cikin aminci ta yanar gizo, wanda ake kira ‘yahoo-yahoo.’

Matasan dai masu shekaru daga 17 zuwa 25, an kamasu ne a ranar Asabar da ta gabata, biyo bayan rahoto da masu leken asiri suka samu dangane da aikin aika-aika da matasan keyi.

Rahoto ya tabbatar da cewar matasan na rayuwa ta manyan yara, wajen siyan sutura da motoci masu tsada, wanda babu wata sana’a da su keyi da zata basu kudi masu yawa kamar hakan.

An samu kwace kayayyaki masu tsada kamar su wayar hannu, kwanfutar hannu, kana da zunzurutun kudade, za’a gurfanara da matasan a gaban kuliya bayan kamala binciken.