Milliyoyin Mutane A Kasashe Matalauta Na Amfani Da Sadarwar Zamani

Hukumar sadarwa ta kasa-da-kasa ta fitar da rahotan cewa Miliyoyin mutanen kasashe mafi fama da talauci a fadin duniya, yanzu suna da hanyar shiga yanar gizo da mallakar wayoyin zamani.

A wannan zamani yana da matukar wahala mutum ya yi harkokinsa ba tare da amfani da kayayyakin fasaha ba, kamar shiga yanar gizo, ko wayyoyin zamani da sauran na’urorin fasaha.

Sabon rahotan da hukumar sadarwa ta kasa da kasa ta fitar, na nuni da cewa ba a kasashen dake da karfin tattalin arziki ne kadai ake harkokin banki da kasuwanci ta yanar gizo kadai ba.

Ta ce baki daya kasashe masu tasowa 47 a duniya suna samun ci gaba wajen samun yanar gizo. Hukumar ta ce sama da kashi 60 cikin 100 na kasashe masu tasowa suna samun fasahar 3G.

Ya zuwa karshen shekara da ta gabata, kusan mutane miliyan 700 a kasashe masu tasowa su kayi rijistar wayar salula, da kashi 80 na mutanen suna zaune a yankunan da wayoyin zamani zasu iya aiki. Ganin wannan ci gaban da aka samu, rahotan hukumar na kan tafarkin cimma muradun karni da Majalisar Dinkin Duniyar ke son cimma zuwa shekarar 2020, na samar da yanar gizo mai rahusa ka kowa.