Wayoyin Android Na Cin Amanar Mutane, Da Mika Bayanan Sirri Ga Google

Mafi akasarin wayoyi masu amfani da manhajar Android, na daukar bayanan mutane da mika su ga kamfanin Google, koda kuwa tsarin nuna bayanan mutun a kashe yake a wayar shi.

Kamfanin jaridar Quartz, suka bayyanar da wannan rahoton, dake bayyanar da cewar duk wasu wayoyin android, na nadar bayanan mutane a yayin da suke kusa da Ariyar kamfanoni waya, da kuma aika duk bayanan ga shafin Google.

A cewar wani manazarcin hakkin bil’adam, ya bayyanar da wannan a matsayin “Cin amana” su kuwa kamfanin na Google, sun tabbatar ma gidan jaridar na Quartz da cewar, basu ajiye wadannan bayanan, kuma zasu yi gyara a na’urorin su don su daina karbar wadannan bayanan.

Matsalar dai na shafar wayoyin android ne da suke dauke da tsarin ‘Google Play’ idan yana kunne a wayar su, dama dai shi tsarin Google play, anyi shine don ya dinga daukar bayanai, musamman wadanda suka shafi manhajoji a wayoyin mutane.

An dai iya gano cewar mafi akasarin wayoyi masu amfani da manhajar android, sun kwasar bayanan mutane wadanda suka hada da inda mutun yake a kowane lokaci, daga bisani suke aikama kamfanin Google.