Kimanin gidajen jaridu saba’in da biyar ne, tare da hadin gwiwar kamfanoni kamar su Facebook, Twitter, da Google, suke wani yunkuri, don yaki da labaran karya da akan yada a kafofin yanar gizo.
Taron da suka yima take “Tsarin Gaskia” “Trust Project” a turance, taron ya gudana ne a birnin Santa Clara, a jihar California ta kasar Amurka. Don fito da wasu hanyoyi da mutane zasu iya gane duk wani labarin karya.
A wannan karni na ashirin da daya, wanda yayi dai-dai da cigaban kimiyyar zamani, yana da wuya a iya tantance labari ko wasu tallace-tallace na gaskiya. A cewar Mr. Sally Lehrman, farfesa a Jami’ar Santa Clara, hakan ya kara sa dar-dar a zukatan mutane, wajen gasgata duk wani labari da suka gani.
Sabon tsarin dai zai bada damar saka alamar “i” ga duk wani labari da mutun ya gani, da kuma tabbacin tushen labarin, kana da wanda ya buga labarin. Ta haka mutun zai iya gasgata labarin idan yaga wannan alamar.
An dai soki kamfanonin Google, Facebook, da Twitter, wajen yada labaran karya, musamman a yayin zaben kasar Amurka da aka gabatar a shekarar da ta gabata 2016, wasu daga cikin labaran da kasar Rasha ta kirkira.
A farkon wannan watan ne dai kamfanin Twitter, suka shaida ma majalisar dokoki ta Amurka, cewar sun rufe kimanin shafufukan karya 2,752, don tabbatar da gaskiyar labaran da mutane ke sakawa a shafufukan su.
Hakan zai taimaka wajen kawo karshen labarai marasa tushe, idan ana rufe shafufukan yanar gizo da basu da asali.
Facebook Forum