Masu iya magana kance “Dare daya Allah kanyi bature” Mr. Loren Krytzer, tsohon kafinta ne da ya kwashe shekaru yana aiki, kuma ya samu abun duniya, kamin wani hadari da ya same shi a shekarar 2007.
Inda ya kwashe tsawon shekara daya kwance a asibiti, wanda daga bisani saida aka yanke mishi kafa daya. Yayi jinya wanda hakan yasa ya rasa aikin shi, ya shiga cikin mawuyacin hali a rayuwa.
Har sai da ya kai ga baya iya lalurar ‘ya'yan shi, hakan yasa ya maida su hannun kakar su. A cikin mawuyacin hali da yake, wanda gwamnati ke bashi kudin haya da na cin abinci da shi da matar shi.
Wata rana yana kallon talabijin, sai yaga wani mutun ya kawo tsohon bargon shi an siya akan makudan kudade, dallar Amurka $500,000, kwatankwacin naira milliyan dari da tamanin.
Hakan ya tuna mishi da wani tsohon bargo da kakar shi ta mutu ta bar mishi gado, wanda aka kiyasta shekarun bargon sun kai shekaru dari biyu da ashirin 220, ya dauki bargon don kaiwa kasuwa.
A dai-dai lokacin da aka duba bargon sai aka iya gane cewar, wannan tsohuwar ajiyace, a karshe dai an siya bargo akan kudi dallar Amurka milliyan daya da dubu dari biyar $1.5M dai-dai da naira milliyan dari biyar da arba’in.
Yanzu haka dai wannan mutumin, ya fara sabuwar rayuwa da shi da iyalan shi, inda suka siya sabon gida, da sababbin motoci, don more sabuwar rayuwar su. Ya bayyanar da jin dadin shi da wannan bargon ya kawo mishi, a lokacin da yake zantawa da manema labarai.
Facebook Forum