Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Gabda Kera Motar Gingimari Mai Amfani Da Hasken Rana


Kimanin fiye da shekaru ashirin da suka wuce, kamfanin Tesla, na kera motocin hawa don jin dadi, wanda har a kwanakin baya sun kera wasu motoci masu aiki da hasken rana.

Kamfanin na Tesla, sun kera sabuwar motar su ta gingimari dake amfani da hasken rana a karon farko, a cewar shugaban kamfanin Mr. Elon Musk, wannan katuwar motar na iya tafiyar kimanin mil dari biyar 500.

Tafiyar da za tayi dai-dai da nisan Lagos zuwa Abuja, batare da ta bukaci karin caji ba, wannan wata sabuwar hanyace ta rage kudin mai, kuma tana da saukin lalura, ga rashin gurbata yanayin iska.

A cewar Mr. Musk, duk wanda yake bukatar motar, zai iya biyan kudi da suka kai dallar Amurka $5,000 kwatankwacin naira milliyan biyu, don za’a fara saida motar idan Allah ya kai rai cikin sabuwar shekarar 2019.

Ya kara da cewar, lallai suna da tabbacin wannan itace motar da tayi dai-dai da zamani, ganin yadda duniya ke canzawa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG