Kamfanin Tesla Zasu Gwada Gingimari Mai Tuka Kanta A Kan Titi

Shahararren kamfanin kasar Amurka, masu kera motoci masu amfani da hasken rana, ‘Tesla’ na kusa da daura babbar motar da suka kera, mai amfani da hasken rana akan titi don gwaji. Ita dai motar tana tuka kanta ne, batare da matuki take tafiya dauke da kaya ba.

Kamfanin na tattaunawa da hukumar kula da tsarin motoci na birnin Nevada, a kasar Amurka, don duba da tabbatar da yadda tsarin zai kasance akan hanyoyi mallakar gwamnatin jihar.

A farkon shekarar nan ne dai aka ruwaito cewar, shugaban kamfanin Mr. Elon Musk, yana cewar a watan Satumbar bana ne suke sa ran kaddamar da gingimari mai amfani da hasken rana.

Duk dai da cewar a bayanin shi, bai furta cewar motar zata zama mai tuka kanta bane, mafi akasarin manyan motoci da suke hawa manyan hanyoyi sukanyi tafiya cikin tsanaki.

Mafi akasarin hanyoyin basu da kwane-kwane, hakan yasa motoci masu tuka kansu zasu iya tafiya akan manyan tituna batare da wata matsala ba. Da yawa akasarin manyan kamfanoni da suka hada da Volvo, Mercedes, suna yunkurin kera irin wadannan motocin.

Ko dai an samu nasarar kammala wannan motar, za’a cigaba da fuskantar matsalolin rashin yawan motoci masu amfani da hasken rana. Shi yasa camfanin Tesla ke kokarin kawo karshen matsalar kamin tayi yawa.