Sojojin ruwan kasar Australia, sun bada tabbacin tsinto burbushin jirgin saman kasar Amurka, wanda yayi layar zana a cikin teku ranar Asabar. A cewar ministan tsaro na kasar Australia, Mr. Marise Payne, yace sun iya gano jirgin a cikin karkashin ruwa, jim kadan bayan fadawar shi cikin tekun.
Ya kara da cewar suna amfani da sojojin ruwa a cikin teku don gano inda sauran jirgin da mutane ciki suke. A kwai mutane ashirin da uku kana da matuka uku da suke cikin jirgin kamun fadawar shi cikin teku.
Ya zuwa yanzu dai, an ceto mutane ashirin da biyu, inda ake cigaba da neman sauran matuka jirgin su uku. Gwamnatin kasar Amurka, ta kaddamar da aikin bincike wajen kokarin gano sauran mutannen, da abun da ya haddasa hadarin.
An dai sanar da iyalan matuka jirgin da ba’a gansu ba, jirgin ya taso daga kasar Australia ne, biyo bayan kammala wani atisaye da akayi na hadin gwiwa tsakanin sojojin kasar Australia dana kasar Amurka, na tsawon mako biyu.
Atisayen da ya hada da sojojin dubu talatin 30,000 da jirage dari biyu 200, mafi akasarin sojojin da suke aikin kwantar da tarzoma ne a kasar Afghanistan da Iraq.
Facebook Forum