Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amfani Da Na'urar Zamani A Zaben Kasar Kenya Wajen Magance Magudi


Taron kungiyoyi masu zaman kansu a kasar Kenya, sun dau alwashin anfani da na’urorin kimiyya da fasaha, don bibiya ga zaben shugaban kasar da za’a gudanar a gobe idan Allah ya kai rai. Kungiyoyin da suka hada da kungiyoyi masu zaman kansu da kare hakkin bil’adama.

Sun samar da matasa ‘yan sakai dubu biyar da dari bakwai 5,700, wanda aikin su shine, su dinga bibiyar yadda zabe ke gudana a kasar baki daya, ta hanyar amfani na’urorin zamani.

A cewear shugaban taron gamayyar kungiyoyin Mr. Simon Wanjiru, wannan kungiyar tasu bata ‘yan siyasa bace, don haka zasu gudanar da aikin su batare da nuna wariya ba. Domin kuwa tun a shekarar 2010, suka fara irin wannan aikin.

Ya kara da cewar, za suyi amfani da na’urorin nan ne don ganin ba’ayi magudi ba a lokaci da bayan zabe ba, hakan zai bama mutane kwarin gwiwar amsar sakamakon zaben idan an fitar da shi bayan zabe.

Haka suna kara shaidama jama’a cewar, za suyi aikin su tukuru batare da ha’inci ba, zasu tabbatar da cewar ‘yan sa kai sun isa duk wata runfar zabe da kayan aiki, wanda zasu dinga aikawa da sakon gaggawar abun dake gudana a runfar da suke.

Hakan zai taimaka matuka wajen hada sakamako a karshe, ganin cewar idan aka samu wani akasi, tsakanin abun da malam zabe suka kawo da abun da ‘yan sakai suka kawo, hakan zai saka alamar tambaya. Daga nan za’a iya bincike don tabbatar da gaskiayar sakamakon kowace runfa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG