Motoci masu amfani da hasken rana na kara karbuwa a fadin duniya. Kamfanoni masu kera motocin na kara inganta su, kana da samar da su cikin farashi mai rahusa. Kamar motar ‘Chevrolet Bolt’ wadda shahararren dan Najeriya Jelani Aliyu ya fara zanawa, haka itama motar ‘Tessla Model 3’
Kasar China na yunkurin yawaita motoci masu amfani da hasken rana, don kara magance matsalar dumaman yanayi da ake kara samu a duniya, sanadiyar yanayi da ababen hawa ke haifarwa.
Tuni kasashen turai suka dau alwashin kawo karshen amfani da motoci masu amfani da Fetur ko Gas, a kasashen nan da shekarar 2040 ko kasa da hakan. Tsarin wadannan motocin na kara samun cece-kuce, wanda mutane ke kara nuna damuwar su dangane da yadda za'a dinga cajin motocin a yayin tafiye-tafiye.
Yanzu haka dai ana kara fadada wuraren cajin motocin, a manya manyan garuruwa da tituna, idan aka duba yadda kasashe kamar su China, Netherland, da kasar Amurka, an samar da wajen cajin motocin a duk wasu gidajen mai da matattarar mutane.
Hakan zai taimaka mutane da suke amfani da irin motar wajen cajin su cikin sauki, batare da sun shiga cikin matsalar rashin caji da motar zata tsaya a tsakiyar daji ba.
Motocin kanyi tafiya da takai ta tsawon kilomita 300, batare da tsayawa ba, don bukatar caji, nan bada dadewa ba wadannan motocin zasu yawaita a fadin duniya.
Facebook Forum