Google yana aiki da tawagar masu kirkirar fasahar kamfanin wajen kirkirar sabuwar fasahar da ake kira Stamp, wadda za a iya amfani da ita wajen wajen samun labarai daga wayar hannu, wadda ke kama da fashar da manhajar Snapchat.
Fasahar Stamp ta samo asali ne daga wata fasaha da Google ya kirkira a baya da ake kira AMP, wadda ke taimakawa wajen kwaso labarai cikin gaggawa zuwa wayoyin hannu.
Yayin da Snap ke ci gaba da kirkiro sabbin hanyoyin sadarwa ta wayoyin hannu, Facebook na bibiya yana kwafar fitattun fasahar kamfanin Snap.
Sai gashi shima kamfanin Google na bibiyar fasahar kamfanin Snap. Snap dai ya jima yana canje-canje a yawancin fasahohin da ya kirkira, wanda yanzu haka ke kan shirin mayar da hankali kan hotunan bidiyo.
Hannun jarin kamfanin Snap dai ya fadi bayan da mujjallar The Wall Street Journal ta fitar da rahotanta, amma daga baya ya daga sama.
Facebook Forum