Kamfanin 'Alibaba' Sun Kaddamar Da Sifika Mai Dan-Karan Wayo

Shahararren kamfanin kimmiya da fasaha na kasar China ‘Alibaba’ sun kaddamar da sabuwar fasahar su ta ‘Smart Speaker’ sifika mai dan-karan wayo. Sun kayata wannan sifikar da ilimin fahimtar muryar mutun, da fuska a yayin ganawa.

Sifikar na magana da mutun a duk lokacin da mutun ya bukaci hakan, za’a iya zantawa da ita, ko bukatar ta bama mutun wani labarin abun da ya taba faruwa a baya. Ana iya umurtar sifikar da ta saka wasu wakokin mawaka da mutun ke sha’awa.

Haka zalika a duk lokacin da mutun yake bukatar siyan abinci, da sanin gidajen abinci da suke kusa da irin nau’o'in abincin da suke siyarwa, mutun zai iya tambayar sifikar, don ta sanar da shi ire-iren abincin da zai samu a kusa.

Kuma mutun zai iya umurtar sifikar, da ta aika ra’ayin mutun na siyan abincin, a duk lokacin da mutun ya bukaci siyan wani abu, zai shaidama sifikar, zata gayama shagon da ake siyar da irin abun da mutun ya keso.

Bayan aikawa da bukatar mutun, za’a kawoma mutun abun da ya bukata har gida. Wannan wata fasahace da aka tserema sauran kamfanonin kimmiyya da fasaha, duk dai da cewar kamfanin Apple, Samsung da makamantan su suna nasu yunkurin wajen ganin sun samar da tasu fasahar da tafi wannan.