Hamshakin kamfanin wayoyin ‘Apple’ sun dauki kwararan matakai wajen inganta wayoyin su da tsaro mafi nagarta a duniyar wayoyi. Dama da jimawa wayar kamfanin Apple suna daya daga cikin wayoyi da satar bayanai ke da wuya.
Wannan sabon tsarin ya biyo bayan matsalolin satar bayanai da aketa fama da shi a kasashen daular larabawa. Musamman idan akayi la’akari da yadda aikin ta’addanci ke karuwa a yankunan.
Masana sun bayyana cewar wasu ‘yan kuntse sunyi amfani da wasu damammaki uku, wajen ganin sun ratsa tsarin tsaro na kamfanin wayoyin Apple, don satar bayanai, amma ba suyi nasara ba.
Kamfanin dai suna bama ma’abota hurda dasu, gwarin gwiwa cewar sun kara inganta tsaro na duk wata wayar kamfanin su, da tabbatar da cewar babu wani dan kutse da zai iya shiga wayoyin mutane don satar bayanai.
Facebook Forum