A watan Afrilu da ya gabata ne, kamfanin ‘Google’ suka kaddamar da wata sabuwar manhaja, mai suna ‘Google Earth’ ‘Taswirar Duniyar Google’ wadda ke dauke da wasu ingantattun hanyoyin kayatar da tsarin.
Sabuwar Taswirar na iya bada dama wajen yawon duniya, da ganin yadda wurare suke a fadin duniya, duk ta hanyar amfani da wayoyin hannu ko naurar kwamfuta.
Mutun na iya sanin yadda tsarin wasu wuraren tarihi suke a fadin duniya, da bada labarin yadda suke, duk batare da mutun yata ziyartar wuraren ba a zahirance.
Yanzu haka kamfanin sun kaddamar da sabon tsarin, manhajar ta makarantun, inda dalibai zasu iya yawon duniya ta yanar gizo. Tsarin mai taken ‘Voyager’ sunan na nufin, ‘Yawon Duniya A Yanargizo’
Sabon tsarin zai ba dalibai damar zagaye duniya a matakin 360, tare da ganin tsarin tituna a ko wace nahiya a duniya. Miliyoyin dalibai a fadin duniya, zasu iya amfani da sabuwar manhajar, don gudanar da binciken kimmiya da fasaha a yanargizo.
Hakan kuma zai zurfafa fahimtar dalibai wajen fahimtar tsarin duniya, dama yadda wasu garuruwan suke a fadin duniya.
Facebook Forum