A shirinmu na nishadi bayan dawowa daga hutun watan Azumin Ramadan da Sallah karama DandalinVOA ya faro ne da Bashir Mai Shadda matashin mai shiryawa da kuma bada umarni a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood wanda ya ce sha’awa ce ta ja shi ga harkar fim da farko.
Ya faro ne bayan ya fara abota da wasu daga cikin gaggan masu shirya fina-finai Kannywood , bayan yawaita zuwa kasuwar kofar wambai domin lalabo sabbin fina-finai da zai saya domin kallo.
Ya ce ya fara ne da Darakta Hafizu Bello, wanda ya fara da wani fim din sa mai suna bincike wanda shine fim dinsa na farko, ya ce tun mutane na bashi kudinsu ya shirya musu fim har ta kai da yana fidda kudi daga aljihunsa domin ya dauki nauyi.
Da farko kamar kowa kalubalen da ya fuskanta dai a farko shine wasu masu shirya fina-finai basu da amincewa da shi ta hanyar rashin son su ga ana damawa da shi ko makamancin haka, amma da taimakon Allah har ya zarce yadda ake zatonsa.
Abubakar Mai Shadda dai ya ce ya samu nasarori da dama cikin har da award din AMVC na best indigenious Hausa Movie, ya kuma sauke farali a ta sanadiyar fim, kuma har kawo yanzu ko auren fari bai yi ba amma ya samu nasara a rayuwa.
Mai Shadda wanda yake matakin karatu na uku a jama’a ya ce a gaba yana da burin bayan kamala digirinsa na farko zai koma makaranta domin samun wani ilimin a fanin fina-finai.
Facebook Forum