Mawakiya Janet Jackson Zata Shiga Duniya Bayan Hutun Iyalai

Mawakiya Janet Jackson

Shahararriyar mawakiya, kuma kanwa ga fittacen mawakin duniya Machiel Jackson. Janet Jackson, ta bayyanawa masoyanta cewar, zata koma fagen waka idan Allah ya kai rai. Biyo bayan hutu data dauka don haihuwar danta na farko.

Ta aika da sakon ta bidiyo, inda ta kara jaddada gaskiyar maganar cewa, aurenta yana kokarin mutuwa, da hamshakin mai kudin daular larabawa, don haryanzu suna kotu, sanin sakamakon auren sai Allah.

Mawakiyar Janet, mai shekaru 50, a duniya ta dauki hutu daga waka bayan ta samu juna biyu. A watan Janairu ne ta haifi jaririn da aka sama suna Eissa.

Ta kara da cewar, zata cigaba da yawace-yawacen duniya data fara a baya. Tana kara mika godiya ga masoyanta da magoya bayanta.

Tace ta sauya sunan wannan yawon nata, wanda ta kira yawo ‘State of the World’ a turance, matakin duniya. Ta kara da cewar a ranar 7 ga watan Satunba na wannan shekarar, take sa ran fara yawon daga jihar Louisiana, ta kasar Amurka.