A makon da ya gaba ne aka gudanar da zaben kungiyar masu shirya fina-finai na Hausa ta kasa wato MOPPAN inda Abdullahi Maikano daga jihar Kaduna ya lashe zaben.
Yayin da mataimakin shugaba ya fito daga jihar Plateau wato Salisu Mu’azu ,sai sakataren Ahmad Alkanawi daga Kanon Dabo .
An dai gudanar da zaben ne a talatainin dare, da misalin karfe 4 na asuba sakamakon wasu shirye-shiryen tantance shugabannin kungiyar ta MOPPAN ta kasa na daga cikin musababbin samun jinkiri da akayi a yayin zaben.
Sakataren hulda da jama’a na kungiyar Murtala Balarabe Baharu, ya ce zaben ya nuna cewa zaben ne na kasa ne ba na wata jihar daya ba, domin ganin irin yadda jami’an, da aka zaba suka fito daga jihohi daban daban.
A cewar sa an samu jagoranci daga jihohin arewancin Nijeriya sannan hakan na nuni da samun cigaba ga harkar fina finai, inda ya ce an kuma sami wasu matsalolin inda wasu daga cikin wadanda suka tsaya takarar suka koka na rashin sanin wasu daga cikin wadanda aka zaba a tafiyar da kungiyar ta (MOPPAN) ta kasa.
Baharu ya ce kwatanta yin zaben nasara ce sannan hanyoyin da aka bi wajen gudanar da zaben ma wata nasara ce.