Na rera wakar marayu ne sanadiyar wata rana, a lokacin da nake yi wa kasa hidima a jihar Bauchi. Na tafi jihar Yobe don ziyartar sansanin 'yan gudun hijira inda na ci karo da ire-iren matsalolin da suke fuskanta, har sai da na zubda hawaye, saoda tausayi inji matashi Kabiru Yusuf Garba.
Ya ce ganin halin da marayu ke ciki ne ya jefa shi cikin tunani da damuwa, da kuma yanke hukunci hanya daya da zai isar da irin mawuyanci halin da suke ciki ta hanyar waka.
Ya ce ya gayyato shahararriyar mawakiyar Hausa Maryam Sangadale, wadda keda buri da damuwa na halin da marayu ke ciki, muka kuma rera tare, tare da bukatar alu’umma da su taimakawa marayu kada a barsu su lalace.
Ya ce rashin kula da marayu shi ke jefa su cikin mawuyaci halin, da zaman manyan gobe da ke damun alumma ta hanyar bangar siyasa, shaye-shaye da sauransu.
Ya ce ya fara waka ne sanadiyar yawan karance-karance da yake yi, ta hanyar rera waka ga dukkanin abinda ya faru da shi.