Masu iya magana kance “Duk wanda ke raye, yana tare da ganin abubuwan mamaki” A wannan karni na ashirin da daya 21st, ana kara samun cigaba, musamman a bangaren kimiyya da fasaha. Kamfanin Google tare da hadin gwiwar kamfanin Levis, kamfani masu dinka kayan sawa.
Babban yunkurin su shine, su samar da wata riga da za’a hada ta da wayar hannu ta Bluetooth. Rigar na aiki kamar yadda mutun zai taba wayar hannun shi, idan kuma mutun ya hada wayar da rigar zai taba rigar sai ta kai sakon duk abun da mutun ke bukata a wayar shi, muddun idan mutun ya hada ta hanyar Bluetooth.
Yadda rigar take aiki da waya shine, idan mutun yana bukatar kunna waka a wayar shi, sai ya taba rigar shi sau biyu, haka idan mutun nason duba lokaci, ko amsa waya da kokarin kiran wata lamba, duk zai iyayi ta taba riga ko dai sau biyu ko sau uku da yatsu biyu ko daya.
A lokacin saka rigar an saka wasu na'urori a cikin zaren, da aka dinka rigar da shi. Hakan kuma bazai hana mutun wanke rigar ba idan tayi datti. Rigar zata isar da duk wani sako, da aka aika ta hanyar taba ta, an kiyasta kudin rigar zata iya kaiwa dallar Amurka $350 kwatankwacin naira dubu dari da sittin.