Alamu na kara nuni da cewar nan gaba kadan mutun mutumi “Robot” zai maye gurbin mutane a wajajen ayyuka da dama, bama kawai a kasashen da suka cigaba, harma da kasashen da ke tasowa.
A kasar Philippen, wasu matasa sun samar da wani kamfani da suke ayyuka da dama, da suka hada da sadaukar ma’aikata na wasu kamfanoni da samar da dangantaka tsakanin kamfanoni, ta hanyar magana da ma’aikata wanda ake kira “customer care” a turance.
Yanzu haka kamfanin ya fara amfani da mutun-mutumi, wajen gudanar da wadannan ayyukan, wanda hakan zai sa milliyoyin mutane rasa aikin yi. Sai dai ana ganin cewar, idan mutane za suyi amfani da irin baiwar da Allah yayi musu, wajen samo da kirkirar wasu sana’o’I da wasu basu taba yin su ba, ko ba’a gabatar dasu wajen amfani da mutun-mutumi ba. Domin akwai wasu sana’o’I da sai mutun mai motsi kawai zai iya gabatar da su.
Masana na ganin cewar duk yadda aka kai, sai dai ace mutun-mutumi zai yi aiki tare da mutu. Babu yadda za'ayi mutun-mutumi ya maye gurbin mutun dari bisa dari.