Mutane Rabin Milliyan Ke Mutuwa A Afrika Sanadiyar Cutar Kansa!

Hukumar kiwon lafiya ta duniya a karkarshin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya ta ce, kimanin mutane sama da rabin milliyan ne a Afrika ke mutuwa sanadiyar cutar sankara ko kuma daji a kowace shekara. Mafi akasarin mata na dauke da sankarar mama, wanda su kuma maza suke dauke da matsalar mafitsara.

A cewar Dr. Andre Ilbawi, likita mai kula da cututtuka na hukumar dake da matsuguni a Geneva, yace mafi akasarin abubuwan da ke haddasa cututtuka a kasashen Afrika ba’a cika sanin su ba, amma wasu abubuwa da bincike ya nuna sun hada da maganar shan giya, kiba, da kuma rashin motsa jiki.

A duk lokacin da jikin mutun baya samun motsawa yadda ya kamata, to za’a iya samun wasu kananan cututtuka da suke taruwa a cikin jikin mutum, wanda daga bisani suke haifar da cutar sankarar ko kuma 'cancer' a Turance.

Binciken ya tabbatar da cewar, yawan mata masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki wato 'HIV' a takaice, sun fi yawa a Kasashen Afrkia idan aka kwatanta da na maza masu dauke da cutar. Haka ma idan mutum ba ya la’akari da nau’in abinci da yake ci, zai iya haddasa wasu cututtuka a jiki.