Likitan Agogo Zai Duba Lafiyar Mutun, A Kowane Mataki!

Agogon Apple

Kamfanin Apple, sun kaddamar da likitan agogo, yanzu haka dai mutane na iya dogara da agogon, wajen tantance lafiya a kowane lokaci. Shi dai agogon yana iya sanarma mutun irin yanayin halin da lafiyar shi take ciki.

Agogon na amfani da ruwan zufar jikin mutun, wajen sanin irin halin da jikin yake, haka yana kidaya irin yawan motsin jikin mutun, don sanar da matakin lafiya a jikin dan’adam.

Masana a cibiyar binciken lafiyar dan’adam ta jami’ar Stanford, sun kara jaddada muhimanci amfani da wannan agogo, kodai bai ba mutun tabbacin abun da yake damu shi ba, kamar yadda likita zaiyi ba, amma zai iya bama mutun wasu alamu, masu kusanci da hakan.

Yanzu haka dai masanan suna gabatar da wani bincike, na kara kiyasta aikin agogon, inda suka tara bayanai na mutane sittin, don kara karfafa binciken su. Agogon zai iya sanarwa mutun idan zai kamu da cuta, musamman irin wadanda suka hada da mura.

Agogon yana dauke da wasu manhajoji, da suke iya sanarma mutun, akwai wasu cututuka da suke kusantar jikin shi, don haka sai mutun ya dauki matakai da suka kamata. Agogon zai shaida ma mutun, alamun kamuwa da cuta kamin ta shiga jikin mutun.