Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gashin Kaji Da Tsuntsaye, Yafi Naman Su Amfani Wajen Samun Abun Duniya!


Gashin Tsuntsaye
Gashin Tsuntsaye

Shekaru da dama da suka wuce, ana sarrafa gashin kaji, tsuntsaye, wajen amfani da yawa. Wasu kadan daga cikin abubuwan da akanyi amfani da gashin shine, akanyi rigunan sanyi, katifa, filo, bargo, kana a kanyi amfani da gashin wajen kayatar da wurare.

Sau da yawa mutane kan yanka kaji, da daukar naman kajin batare da amfana daga gashin kajin ba. Yanzu haka dai wasu dalibai dake gudanar da wani bincike, mai zurfi a matakin digirin-digirgir a jami’ar birnin Birtaniya.

Sun gano wata hanyar amfani da gashin kaji, tsuntsaye wajen samar da wasu kayan amfanin yau da kullun na gidaje da ofisoshi. Binciken su ya nuna musu wasu hanyoyi da za’a iya sarrafa duk wani gashin kaji ko tsuntsaye da ke da fiffike.

Tsuntsaye dai Allah, yayi musu wannan gashin ne, don samun kariya daga yanayin zafi, sanyi da duk wani abu da kan iya cutar da su. Yanzu haka suna kokarin samar da hanyar da mutane zasu dinga amfani, da gashin wajen samar da aikin yi da sana’a ga mutane.

Wasu sinadarai da suke amfani da su wajen sarrafa gashin, don samar da kaya da suka hada da robobin kayatar da daki, kayan wasan yara, da dai makamantan su. Amfani da gashin kaji, tsuntsaye na da sauki wajen sarrafawa, don rashin nauyin shi, zai bada damar amfani da sinadarai kadan don samun abu mai yawa cikin kankanin lokaci.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG