Yusuf Abubakar: Arzikin Kowace Kasa, Yana Hannun Matasan Kasar Masu Ilimi!

Yusuf Abubakar

Yusuf Abubakar, dan asalin karamar hukumar Maiduguri dake jihar Borno ne. Wanda ya samu damar karatu tun daga matakin firamari, a makarantar ma'aikatan jami’ar Maiduguri, a cikin birnin Maiduguri. Wanda daga bisani ya samu halartar makarantar sakandire a jihar Yobe. Kana ya samu damar shiga jami’ar Maiduguri, inda ya kammala karatun digiri na farko a fannin ilimin sanin tsibirai, kasa da kuma ma’adanan dake karkashin kasa “Geology” a turance.

Yusuf, yayi bautar kasa a kwalejin tunawa da margayi “Sir Ahmadu Bello Sardauna” dake Kaduna, inda ya koyar da ilimin noma. Bayan kammalawa, ya sake samu damar karo kararu a matakin digiri ta biyu “MSc a bangaren Petroleum Geochemistry” a jami’ar “Newcastle upon Tyne” dake kasar Birtaniya.

Yanzu haka dai Yusuf, yana daya daga cikin zakaru, da suka samu damar koma kasar Birtaniya, don karo karatu mai zurfi, a matakin digirin-digirgir, a birnin Manchester. Yana gudanar da bincike kan sinadaran dake haduwa a cikin karkashin kasa don samar man-fetir “Crude Oil”

Ire-iren binciken da Yusuf, ke gudanarwa a jami’ar da yake, yana daya daga cikin bincike, da aka saka cikin sahun gaba. Hakan kuma ya auku ne a sanadiyar irin hazakar shi, da tsarin karatun da ya samu tun a gida Najeriya.

Yana kira ga matasa da su fahimci cewa sune ginshikin al’umma, saboda haka su sa himma wurin karatu na zamani da na rayuwa, don sune manyan gobe. Idan suka kyautata, babu shakka dukkan al’umma zatayi kyau, idan kuma suka lalace dukkan al’umma zata lalace. Babban fata shine, Allah ya bawa kowa dama da himman karatu.

A karshe kuwa shine, matasa su sani cewa ba lallai bane sai mutun yana da ra’ayin aikin gwammanati ba, kamin yayi karatu boko, kowace sana’a tana bukatar ilimi kuma ba’a samun ilimin sai anyi karatu.